Hukumar Alhazai ta Kasa ta yi kira ga maniyyatan jihar Gombe da su kwana da sanin cewa za a yi amfani da tsarin tantance maniyyata ta kwamfuta.
Shugaban hukumar ne Abdullahi Muhammad, ya bayyana haka ranar Alhamis a garin Gombe, a lokacin da ya ke yin jawabi ga jami’an hukumar da kuma maniyyatan jihar.
Shugaban ya kuma ce wannan sabon tsari cika umarni ne daga kasar Saudiyya. Ya kuma ce duk wanda a baya ya taba zuwa aikin Hajji, to a wannan shekara sai ya biya riyar 2000, kwankwacin naira N163,000 cif kafin ya tafi zuwa kasar.
Shugaban ya ce hukumar sa na bakinn kokarin ta wajen tabbatarwa Hajjin bana bai haura na bara tsada ba.
Ya kuma shawarci duk maniyyaci ta kammala biyan kudaden sa kafin karshen wannan wata na Maris.
Discussion about this post