Gwamnatin tarayya ta maida wa TY Danjuma martani kan kira da yayi “Kowa ya Kare kan sa”

0

A kwanankin baya ne tsohon ministan tsaro TY Danjuma ya yayi kira ga mutanen yankunan da ke fama da rashin zaman lafiya a kasar nan da su dauki makamai domin kare kan su.

Theophilus Danjuma ya zargi sojojin Najeriya cewa su na taimaka wa ana kashe mutane a jihar Taraba da sauran yankuna.

Ya ce sojojin Najeriya su na nuna son kai da bangaranci, inda suke hada baki su na barin mahara na kashe mutane a Taraba da sauran jhohin kasar nan.

Ya yi wannan furucin ne a wurin bikin yaye dalibai a Jami’ar Jihar Taraba, a Jalingo, babban birnin jihar.

Jawabin da ya yi wanda aka watsa a AIT, an yi ta tura furucin na sa a soshiyal midiya inda aka ruwaito ya na cewa jama’a su tashi su kare kan su da kan su.

Danjuma na nuni da cewa sojoji na taimaka wa makiyaya.

Wannan furuci na sa ya janyo masa fushin jama’a a fadin kasar nan, inda tuni da dama ke cewa ya zubar da girman sa, tunda har ya yi kiran da mutane su tashi su dauki makamai da kan su.

“Idan har ku ka zauna galala sai kun jira sojoji sun kare ku, to za a kashe ku daya-bayan-daya.

“Al’ummar Taraba da sauran yankunan Najeriya su tashi su kare kan su da kan su.” Inji Danjuma.

Furucin Danjuma zubar da girma ne -Sojojin Najeriya

Sai dai kuma nan da nan Hedikwatar Sojojin Najeriya ta maida masa kakkausan martanin cewa zargin da ya ke yi karya ne, ba gaskiya ba ne.

Sojojin sun nuna cewa ko kadan basu dauka mutum irin Danjuma zai maida kan sa kasa ya yi irin wannan kasassaba irin wadda sai gogarma ne kawai ke iya yin wannan danyar magana.

Musamman sun nuna rashin jin dadi, ganin cewa ya yi wannan kalami ne a lokacin da su ke kan ganiyar kokarin ganin sun dawo da zaman lafiya ya dore a kasar nan.

” Ya kamata jama’a su sani cewa sojoji ne a sahun gaba wajen sadaukar da rayukan su ana kashe su domin a tabbatar da samun zaman lafiya a Taraba.

Garba Shehu da ya fitar da wata sanarwa kan haka ya ce gwamnati ta yi matukar mamakin fadin haka da Danjuma yayi.

Ya ce a matsayin sa na tsohon dakare sannan wanda yayi gwagwarmawa don hada kan kasar nan bai kamata ace shine yake irin wadannan kalamai ba.

ko da yake gwamnati bata fito karara ba ta bayyana sunan sa, ta yi kira ne ga dukkan masu fada aji da shugabanni a kasar nan da su dinga sara suna duban bakin gatari.

Share.

game da Author