Gwamnatin Sokoto ta raba wa dattawa 200 tallafin kudi da abinci

0

Hukumar Zakka ta Jihar Sokoto ta raba tallafin abinci da kudade tare da magani da kula da lafiya ga wasu dattawa 200 a Karamar Hukumar Gwadabawa da ke cikin jihar.

Shugaban Hukumar ne Lawal Maidoki ya bayyana haka tare da kari da cewa an shirya ci gaba da bayar da wannan tallafin wa hakimai 86 na cikin jihar.

Ya kara da cewa wannan tallafi na daga cikin hanyoyi da dama da gwamnatin jihar Sokoto ke bi wajen nuna kulawa ga marasa karfi a fadin jihar.

Maishanu ya ce tsoffi da dattawa a koda yaushe su na bukatar kulawar da ta wajaba a kan su. Daga nan sai ya yi kira ga masu hannu da shuni da su kai dauki wajen tallafa wa annan shiri.

Ya ce wannan tsari da aka fito da shi, ya na daya daga cikin tsare-tsaren da suka wajaba hukumar zakka ta rika aiwatarwa ga marasa karfin cikin al’umma.

Maidoki ya ce an raba wa dattawa 200 da aka tsamo daga kananan hukumomin Gwadabawa da Kware, inda aka raba musu abinci, tabarmi, sutura da kudi naira 5,000 kowanen su.

A jwabin sa, Gwamna Tambuwal, wanda Kwamishinan Harkokin Addini, Abdullahi Maigwandu ya wakilta, ya jinjina wa hukumar saboda wannan dauki da ta kai na rage wa dattawa radadin kunci rayuwa.

Share.

game da Author