A farkon makon nan ne gwamnatin jihar Neja ta raba Naira biliyan daya wa masu kananan sana’o’I su 11,578 a shirin ta na tallafa wa masu kananan sana’o’i a jihar.
Gwamnan jihar Abubakar Bello ya bayyana cewa gwamnati ta yi haka ne domin gina masu kananan sana’o’I da ke fama da karancin jari a kasuwancin su.
” Wannan wata dabara ce da zata taimaka wajen kawar da zaman kashe wando tsakanin matasa ta hanyar samar musu da aikin yi wanda daga nan zai gina jihar gaba daya.”
Bello ya yi kira ga wadanda suka sami wadannan kudade da su mai da hankali kwarai wajen ganin sun yi amafani dasu kamar yadda aka basu sannan su tuna cewa bashi ce aka basu.
A karshe shugaban kungiyar masu kananan sana’o’I na jihar Farouk Audi yace sun zabo mutane 11,578 daga duk kananan hukumomin jihar wanda 6,343 daga cikin su mata ne sannan 5,244 maza.
Ya ce wannan shiri zai taimaka wajen kawar da talauci tsakanin mutane, kawar da miyagun aiyukka sannan da gina jihar baki daya.