Gwamnatin Katsina za ta horas da ‘yan jarida sana’o’in hannu

0

A ranar Talata ne gwamnan jihar Katsina Aminu Masari ya yi kira ga manema labarai da su mai da hankali kan darussan sana’o’in hannu da ake koyar da su a kai.

Ya yi tsokacin haka ne a taron horas da ‘yan Jarida 60 daga kungiyar ‘Yan jarida na Najeriya (NUJ) reshen jihar da hukumar samar da aikin yi na jihar (KASEED) ta shirya musu.

Masari ya ce za a koyar da ‘yan jaridar ne yadda ake kiwon kudan zuma, kifi da kaji sannan bayan an horas da su za su koyar da wasu suma.

Masari ya ce gwamnati ta hada guiwa da bankin manoma da babban bankin Najeriya domin samar wa wadanda suka ci maki 40 a jarabawar karshe na koyan sana’ar.

A karshe shugaban kungiyar ‘yan jaridar (NUJ) Bahir Mamman ya mika godiyyar sa ta musamman ga gwamnatin jihar kuma yayi wa gwamnati alkawarin cewa ‘yan jaridar za su yi amfani da wannan dama domin inganta rayuwar su.

Share.

game da Author