Gwamnatin Adamawa ta horas da matasa 10,000 sana’o’in hannu

0

A yau ne gwamnan jihar Adamawa Mohammed Bindo ya bayyana cewa gwamnatin sa ta horas da matasa 10,000 sana’o’in hannu a jihar.

Ya fadi haka ne a taron horas da masu tuka keke NAPEP wanda kamfanin ‘Simba Groups’ ta shirya a Yola.

Bindow yace sun yi haka ne domin samar da aikin yi da kawar da zaman kashe wando a tsakanin matasan jihar.

” Cikin sana’o’in hannun da muka koyar sun hada da aiyukkan noma sannan mun samar musu da jari.”

A karshe shugaban kamfanin ‘Simba Groups’ Manish Rotahagi ya jinjinawa gwamnan jihar kan gyara hanyoyin jihar da ya yi cewa gyaran zai taimakawa wajen hana saurin lalacewar ababen hawa.

Share.

game da Author