Gobara ta lashe shaguna 600 a kasuwar Bida

0

Shugaban karamar hukumar Bida a jihar Neja Mohammed Badugu ya bayyana cewa gobara ta lashe shaguna 600 a kasuwar Bida jihar Neja.

Ya fadi haka ne da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai Najeriya (NAN) ranar Juma’a inda ya kara da cewa gobarar ta fara ne da misalin karfe 8:30 na yammacin ranar Alhamis.

Badugu ya ce ma’aikatan kashe gobara na Bida da na kwalejin kimiya da fasaha dake garin Bida ne suka taimaka wajen kashe gobarar.

Badugu ya ce duk da cewa gobarar ta yi sanadiyyar rasa dukiyoyin ‘yan kasuwa karamar hukumar za ta yi kokarin gana sabon kasuwan cikin dan kankanen lokaci.

Share.

game da Author