Gobara ta lashe shaguna 22 a kasuwar Kano

0

Jami’in harka da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano Sa’idu Mohammed ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa gobara ta lashe shaguna 22 a kasuwar ‘Yankatako dake Rijiyar Lemo a jihar.

Mohammed ya ce wani mazaunin unguwar kurna ne mai suna Muhammed Yahaya ya sanar da hukumar da misalin karfe 3:10 na safiyar Laraba.

” Daga nan sai muka dauki motocin mu da kayan aiki muka nausa wannan kasuwa, isar mu ke da wuya kuwa muka far ma wutan har Allah ya sa ta mutu murus.”

A karshe Mohammed yayi kira da a yawaita maida hankali da kayan wuta a kasuwanni da gidaje sannan ya shawarci mutane da su ajiye na’urori da ababen kashe gobara na zamani kusa da su domin gudun yawaita asara.

Share.

game da Author