Gobara ta lashe katafaren dakin gwajin cututtuka na Asibitin kula da masu dauke da cutar Tarin Fuka dake Zariya

0

Shugaban dakin gwajin cututtuka na katafaren asibitin kula da masu dauke da cutar tarin Fuka dake Zariya, Labaran shehu ya shaida wa kamfanin dillancin Labaran Najeriya cewa dakin gwajin asibitin ya babbake kurmus sanadiyyar wuta da ta tashi cikin dare a asibitin.

Ya ce sai da wutar ta dauki awoyi hudu tana ci kafin masu kashe gobara suka shawo kan sa.

A wannan asibiti ne dai ake yin gwajin cutar tarin fuka, cutar kanjamau, da zazzabi Typhoid.

Share.

game da Author