Jam’iyyar PDP ta bayyana wannan sunaye da jam’iyyar APC ta jero na wasu jiga-jaigan jam’iyyar ta cewa sune suka sace wasu makudan kudade a kasar nan a lokacin da take mulki.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, ya ce idan bera da sata daddawa ma da wari, kamar yadda ake yi wa ‘ya’yan jam’iyyar lakani da barayi, suma jam’iyya mai mulki ai ba kanwar lasa bane.
Idan ba a manta ba jam’iyyar APC ta fitar da jerin sunayen wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP da yawan kudin da suka zaftara.
A martani da ta maida wa APC, ta ce lallai ta iya wa bakin sa sannan idan tone-tone suke so ayi, ga fili ga doki, ” Mu zuba mu gani”
Daga nan sai ya fara bankado wasu harkalla da akayi ta tafkawa a wannan gwamnati mai ci.
” Ina bayanin badakalar tsohon sakataren gwamnatin tarayya, David Babachir, sannan ina maganar naira biliyan 10 da ya bace bat a hukumar inshorar lafiya ta kasa, sannan ina maganar harkallar miliyoyin daloli da suka bace a wasu harkallar shigo da mai da ma’aikatar man fetur ta kasa tayi da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC ke da hannu dumu-dumu.