Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, John Oyegun ya bayyana cewa jam’iyyar za ta yi amfani da duk wani abin da za ta iya yi domin ta ci zaben gwamnan jihar Ekiti, wanda za a gudanar cikin 2018, a ranar 14 ga Yuli.
Oyegun ya yi wannan furucin ne a sakatariyar jam’iyyar APC, lokacin da ya je Ado-Ekiti, babban birnin jihar domin ya kaddamar da shirin yin rajistar jam’iyyar APC a jihar. Ya ce ‘tilas fa sai APC ta ci wannan zaben mai zuwa.’
Ya bada tabbacin cewa APC za ta gudanar da zaben fidda-gwanin dan takarar gwamna a cikin adalci ba tare da magudi ba.
Ya ce da jerin sunayen wakilan mazabu, wato ‘delegates’ za a yi amfani da ba tare da magudi ko karfa-karfa ba.
Ya ce, “duk da APC ce ke mulki a tarayya, wannan ba zai sa Shugaba Muhammadu Buhari yayi magudi a zabe ba.
“Amma fa za mu yi amfani da karfin mu domin tabbatar da cewa tilas mun yi nasara.”