#DAPCHI: Gwamnati ta ci amanar mu, inji mahaifin yarinyar da ta rasu

0

Mahaifin daya daga cikin daliban Dapchi da ta rasa ran ta sakamakon tirmitsitsi a cikin mota lokacin da Boko Haram suka sace su, ya bayyana cewa su dai a jikin su su na jin cewa gwamnatin Najeriya ta ci amanar su.

Magidancin mai suna Adamu Jumbam, ya bayyana cewa maganar gaskiya shi dai bai ji dadin yadda gwamnatin Najeriya da jami’an tsaro suka tafiyar da batun ba, ya na mai dora musu laifin mutuwar ‘yar sa, mai suna Aisha Adamu.

Daga cikin daliban mata 110 da Boko Haram suka sace, sun maida 104, wasu 5 kuma sun mutu, sai guda daya da suka rike saboda a cewar rahotanni daga daya daga cikin matan, ta ki rika saka hijabi, kuma an nemi ta musulunta, amma ta ki.

A tattaunawar da Jumban ya yi da PREMIUM TIMES, a cikin garin Dapchi, inda ya ke zaman makokin rasuwar ‘yar sa, mai shekaru 16, ya jefa shakku da kokwanto dangane da yadda aka sace yaran da kuma yadda aka maida su Dapchi.

Da ya ke magana ya na kuka, mutumin mazaunin kauyen Jumbam, kilomita biyu daga Dapchi, ya ce “maimakon sojoji su dirar wa Boko Haram, bayan sun ajiye yara sun fita daga garin Dapchi, sai kawai suka rike hannu suka bari su ka fice suka yi tafiyar su.

Adamu bai gamsu da dalilin gwamnati na kin bude wa Boko Haram wuta ba, maimakon haka, sai ya ke fada a cikin fushi tare da kwararar da hawaye a gaban dimbin mutanen da suka je yi masa ta’aziyya cewa cewa, “ya daina yin amanna da gaskata gwamnatin Najeriya.

“An shaida mana cewa sun mutu a kan hanyar tafiya, sannan Boko Haram suka gina rami suka rufe su. Kenan na rasa ta har abada, don haka babu abin da ya rage mana, sai dai mu yi wa wannan baiwar Allah zaman makoki.

“Tun daga ranar da aka sace su na fita hayyaci na ni da mutane da yawa na Dapchi, na yi addu’a, na sha kuka da tunani.

“Ranar da aka dawo da su, ina jin labari sai na runtuma a guje domin na je na karbo Aisha, amma ina zuwa sai aka ce min ai ta mutu a cikin tirmitsitsi.”

Adamu ya ce akwai kumbiya-kumbiya a harkar gwamnati.

“A ce dai Boko Haram su shigo Dapchi da sanyin safiya, su shafe awa daya a tsakiyar kasuwar gari su na yi wa jama’a wa’azi, sannan su fice jami’an tsaro bas u ce musu komai ba har su koma inda suka fito, hakan kamar ya na nuni da cewa gwamnatin Najeriya na yaudarar mu ne kawai.”

Share.

game da Author