#DAPCHI: Abubuwa 29 da suka faru a cikin kwanaki 29

0

1 – Ranar Litinin, 19 Ga Fabrairu, 2018, da misalin karfe 6 na yamma, Boko Haram sun kutsa makarantar sakandaren mata ta garin Dapchi, cikin jihar Yobe, suka arce da dalibai 110.

2 – Bayan sun arce da su, sun yada zango a cikin jeji, inda suka raba wa masu azumin tadawwa’in ranar Litinin kayan buda baki.

3 – Daga nan an sake kwasar su, aka yi ta tafiya har aka je bakin wani gulbi, aka ajiye motoci aka loda yaran cikin kwale-kwale.

4 – Sun tsallaka ruwa, suka yada zangon kwana daya a wani kauye, daga nan safiya na yi suka sake hawan kwale-kwale, suka tsallaka cikin wani jeji mai surkudin duhuwar bishiyoyi. A can ne yaran suka shafe kwanaki 28 ana tsare da su.

5 – Boko Haram sun yi tataburza da wata daliba, mai suna Leah Sherabu, domin ta musulunta, amma ta ki, dalili kenan ba su sake ta ba har yau. Dama kuma an cirza da ita ta rika saka hijabi, amma ta ce atafau. Daliban sun ce ba a tozarta su ba, kuma ba a ci zarafin su ba.

6 – An yi ta tseren dora wa juna laifi tsakanin rundunar ‘yan sanda da rundunar sojojin kasar nan, kowa na cewa daya bangaren ne ke da alhakin sakacin sace yaran.

7 – Gwamnatin jihar Yobe ta yi azarbabin riga-malam-masallaci, inda washegarin ranar da aka sace yaran ta yi sanarwar cewa an gano yaran a cikin jeji.

8 – Manyan jami’an gwamnatin Shugaba Muhammdu Buhari sun yi ta karakainar zuwa jihar Yobe, har garin Dapchi domin tantance gaskiyar magana, shin sace yaran aka yi, ko kuwa sun fantsama jeji ne kowace ta boye.

9 – Shugaba Buhari ya gamu da fushin ‘yan Najeriya, wadanda suka rika ragargazar sa a soshiyar midiya, ganin ya ki nuna damuwa da sace daliban, kwanaki kadan ya halarci daurin auren diyar Gwmnan Kano, Abdullahi Gandu da dan Gwamnan Oyo, Ajimobi.

10 – Matsin-lamba ya sa tilas Buhari ya kai ziyara har a Dapchi, da ma wasu jihohin da kashe-kashe ya ritsa da dimbin jama’a.

11- An rufe makarantun sakandare na kwana na jihar Yobe.

12 – An rika tura jami’an ‘yan sanda da na Civil Defence su na gadin makarantun sakandare a jihohin Yobe da Adamawa da Barno.

13 – An girke sojoji a garin Dapchi.

14 – Cikin wannan sati, Ministan Tsaro Mansir Dan’Ali, ya ce za a dawo da daliban Dapchi ba da dadewa ba.

15 – Hajiya Aisha, Mama Boko Haram ta ce ta san wadanda suka sace yaran, ba bangaren Shekau ba ne.

16 – Ranar 20 Ga Fabrairu, da misalin karfe hudu na dare, mazauna garin Gamsu sun ga abin al’ajabi, yayin da rundunar Boko Haram a cikin kwamba din motoci suka biya kauyen, suka maida musu dalibai mata biyu wadanda ke cikin dalibai sama da 100 da suka gudu da su.

17 – Daga garin Gamsu an tsegunta wa mutanen garin Dapchi cewa su shirya ga Boko Haram nan sun tunkaro garin, dauke da yaran garin da suka arce da su.

18 – Da sanyin asubahi mutanen Dapchi suka rika tserewa daga garin, gudun kada Boko Haram su sake yi musu wata barna.

19 – Iyayen yaran da aka sace ba su gudu ba. Sun tsaya sun karbi yaran su. Har aka rika daukar hoto da Boko Haram da jama’ar gari.

20 – Tun da Boko Haram suka dauko yaran kusan kilomita sama da 200 har Dapchi, ba su ci karo da jami’an tsaro ba.

21 – Sojojin da ke tsaron Dapchi sun janye a bisa umarnin hukuma cewa kada su yi arba ko artabu da Boko Haram.

22 – Motocin da aka sace daliban Dapchi, kwanaki 29 baya, da su ne kuma aka sake maida su gida.

23 – Boko Haram sun yi wa jama’ar gari wa’azi da huduba cewa su guji saka ‘ya’yan su makarantun boko.

24 – Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta bada ko sisi a matsayin kudin ladar maido yaran da aka yi ba.

25 – Yara biyar sun mutu sanadiyyar tirmitsitsi a cikin motoci a daren da aka sace su.

26 – Jim kadan bayan Boko Haram sun fice daga garin da misalin karfe 9 na safe, jami’an DSS sun dira garin, inda daga bisani sauran jami’an tsaro suka isa, aka kwashe yaran aka nufi da su Maiduguri, daga nan aka dauke su zuwa Abuja, duk a rana daya.

27 – Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed, ya ce karfe uku na asubahi, aka saki yaran, su kuma jama’ar Dapchi sun ce karfe 8 na safe Boko Haram suka isa garin suka shafe kusan awa daya a cikin Dapchi.

28 – Boko Haram sun ce su kyale yaran ne domin sun tausaya musu, kuma babu wanda ya biya su ko kwabo. Amma sun gargadi mutanen garin su janye yaran su daga makarantun boko.

29 – An bar ‘yan Najeriya cikin waswasin abin da ya faru. Haka APC da PDP sun rukume sabon rikici, kowane na siyasantar da batun maida daliban Dapchi sama da 100, da Boko Haram suka yi da rana kata, ido-na-ganin-ido. Wasu na jinjina wa gwamnatin Buhari, wasu kuma na kallon abin kamar a majigi.

Share.

game da Author