Dan Najeriya ya kafa tarihin wanda ya fi kowa karanta littafi a duniya

0

Wani dan Najeriya mai suna Bode Olawunmi, ya kafa tarihi, a matsayin mutumin da fi kowa dadewa ya na karatun littafi a bayyane, a zama guda.

Ya fara karatun tun daga karfe 1:30 na ranar Litinin, bai tsaya ba sai karfe 3:30 na yammacin Asabar, kwanaki biyar kenan, a dakin karatu na Yaba, Legas.

Olawunmi mai mata da ‘ya’ya uku, ya yi karatu na tsawon sa’o’I 120 a cikin kwanaki biyar.

Ya kwace kambun rakod na Neepali Deepark Sharma wanda ya yi karatun tsaron sa’o’I 113 da minti 15 a cikin 2008.

Share.

game da Author