Sanata Enyinnaya Abribe daga Jihar Abia, ya soki lamirin Shugaba Muhammadu Buhari kan yadda ko da yaushe bai yarda ya yi laifi ko kuskure.
Abaribe ya ce abin haushi ne duk lokacin da Buhari ya yi kuskure sai ya ce “Ni ban sani ba.”
Abaribe ya bayyana haka ne yau Alhamis a zauren Majalisar Dattawa. Sanatan ya kara da cewa irin kasassaba da soki-burutsun da ke fitowa daga bakin Shugaban Kasa, sun nuna cewa ba ya nuna alamun kamo hanyar da za a magance matsalar rashin tsaro a kasar nan.
“Mu na da shugaba wanda za a wayi gari ya ce bai ma san Sufeto Janar na ‘yan sandan kasa ba ya bin umarnin sa ba.
” Duk shugaban da ka ji ya na cewa bai san wani babban al’amari da ya shafi tsaron kasa ya faru ba, to ku tabbatar da cewa kananan al’amurran ma bai san su na faruwa ba.”
Ya ci gaba da cewa jami’an tsaro sun kasa shawo kan matsalar tsaro saboda jagoran kasar dungurugum shi ma bai san abin da ke faruwa a kasar ba.
Ya kuma yi tsokaci da nuni da irin kasawar da shugabannin jami’an tsaro da na siyasa suka yi har ya bada misali da cewa gwamnan jihar Zamfara ya san za a kai wa jama’a hari, amma ya fice daga jihar ya tafi yawon gallafiri ana dabdala da bulkara da shi.
“Ta yaya shugaba zai iya daukar wani mataki, alhali bai san duk abin da ke faruwa a kasar sa ba? Ya kamata shugaban majalisar dattawa ya roki shugaban kasa ya dauki alhakin duk abin da ya kasa yi. Ya daina cewa shi bai ma san abu ya faru ba. Da haka ne kawai za mu iya jin cewa akwai masu kula da rayukan mu a Najeriya.”