Dalilin da ya sa AG ya fice daga APC duk da kusantar sa da Buhari

0

A shekarar 2011, mazauna jihar Kaduna sun koka kan yadda sakamakon zabe ya kaya tsakanin gwamnan mai ci a wancan lokaci wato marigayi Ibrahim Yakowa na jam’iyyar PDP da Haruna Saeed na jam’iyyar Buhari wato CPC.

Masu yin fashin baki kan al’amurran siyasa a jihar Kaduna sun karkata cewa lallai wannan zabe Haruna ne ya lashe shi an nuna masa fin karfi ne, ganin cewa shine na hannun daman Buhari a jihar a wancan lokaci.

Ya samu ruwan kuri’u a zaben saboda daga hannun sa da Buhari yayi da kuma ganin kusantar sa da Buhari.

Kwatsam an wayi gari ranar Alhamis, Haruna ya sanar da ficewa da ga jam’iyyar APC jam’iyyar da Buhari ke jagoranta.

Jama’a dai suna ganin cewa kusancin sa da Buhari ba zai sa ya iya ficewa daga jam’iyyar da Buhari ke ciki ba.

Haruna wanda aka fi sani da AG ya sanar da haka ne a garin Kaduna inda ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar APC ne saboda rikita-rikitar da take fama da shi a jihar.

Ya ce jam’iyyar APC ta rabu kashi-kashi a jihar sannan bangaren gwamna Nasir El-Rufa’I ne uwar jam’iyyar ta yarda da ita.

A wasikar ficewa daga jam’iyyar APC da Haruna yayi, ya fadi cewa ya mika wa mazabar sa wasikar ficewar.

” Ni Haruna Yunusa Sa’eed a yau ranar 15 ga watan Maris 2018 na fice daga jam’iyyar APC saboda rashin sanin inda jam’iyyar ta dosa na rabuwar kan ‘ya’yan ta a jihar Kaduna.”

Share.

game da Author