Jami’in Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i na Kasa (JAMB) reshen jihar Adamawa Danladi Ayuba ya bayyana cewa dalibai 100 sun ki zuwa rubuta jarabawar da aka fara tun a ranar Juma’ar da ta gabata.
Ya sanar da haka ne ranar Litini yayin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Yola.
Ya ce har zuwa yanzu hukumar bata sami wata bayani game da rashin zuwan wadannan dalibai ba.
” Dalibai 3,115 ne suka yi rajistan jarabawar JAMB din bana amma tun da muka fara jarabawar ranar Juma’a mun gano cewa dalibai 100 ba su zo ba sannan hukumar bata san menene dalilin haka.
Discussion about this post