Dakarun Kwastam sun kama tankin mai make da buhunan shinkafa har 589 a jihar Kebbi

0

Shugaban hukumar kwastam dake kula da shiyar Sokoto, Kebbi da Zamfara Nasir Ahmed ya bayyana cewa dakarun sa sun tsamo buhunan shinkafa 589 a cikin tankin man fetir a jihar Kebbi.

Ya sanar da haka ne ranar Talata a Sokoto da ya ke zantawa da manema labarai inda ya kara da cewa sun kama hade da mutane hudu wanda suke da alaka da safarar shinkafar zuwa jihar.

Ahmed yace sun fara bibiyyar masu safarar shinkafar ne tun daga garin Suleja jihar Neja inda sai da ” muka kai jihar Kebbi ne sannan muka sami nasarar kama su.”

” A lissafe buhunan shinkafar da muka tsamo daga tankin man zai kai ta Naira miliyan 11.1.”

Ya ce wannan shine karo na uku da hukumar ke kama kayan da aka boye a tankin mai wanda hakan ya sa yake kira ga masu aikata rin haka da su nemi aiki na gari su yi.

A karshe ya yi kira ga mutane da su ci gaba da ba hukumar hadin kai don ganin an kawar da baragurbin mutane a kasar nan.

Share.

game da Author