Dakaci ya kashe masu garkuwan da suka zo sace shi da Iyalan sa

0

Dakacen Mayo Selbe dake karamar hukumar Gashaka, Jauro Hammangabdo ya fatattaki wasu masu garkuwa da mutane da suka far masa da Iyalan sa inda ya sami sa’ar kashe biyu daga cikin su.

Barayin sun far wa fadan mai unguwa Jauro ne su tara da daren Laraba, Jin motsin su ke da wuya sai ya jawo takobin sa ya buda. Kafin su ankara ya baras da mutum biyu cikin su.

” Nan take sauran barayin suka jefar da bindigogin su suka ‘ari na kare’.”

Shugaban karamar hukumar Gashaka Mohammed Gayam ya bayyana wa manema labarai cewa a dalilin arangamar da Jauro ya yi da wadannan barayi, sun sare shi a kai da gabobin sa amma mun kai shi asibitin soji da ke Serti inda har ya fara samun sauki.

Share.

game da Author