DA BABU GARA BA DADI: An tsoma ‘Civil Defence’ harkar tsaron Barno, Adamawa da Yobe

0

Tun bayan kalaman da Hukumar Tsaro ta Sojojin Najeriya suka furta cewa ba su iya gudanar da aikin tsaron ilahirin makarantun sakandaren jihohin Barno, Adamawa da Yobe kakaf ba, aiki ya karkata wajen yin amfani da jami’an tsaro na Civil Defence Corps wajen tabbatar da tsaro a wasu muhimman wurare a jihohin biyu.

A nasa bangaren, Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci Shugaban Civil Defence Corps na Kasa, Abdullahi Gana da ya tare gaba daya a jihar Barno domin aikin tura dakarun sa kula da tsaron sakandare a jihohin Barno, Yobe da Adamawa.

A jiya Asabar ne Gana ya isa inda Maiduguri, Kwamandan Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Rogers Nicholas ya tarbe shi a cibiyar tsara dabarun yaki ta Maiduguri.

Tuni dai tun bayan sace daliban sakandare na Dapchi a jihar Yobe, aka tura dakarun Civil Defence 250 su rika kula da makarantu dabam-dabam a fadin jihar.

Share.

game da Author