CUTAR SANKARAU: Mutane 51 sun kamu da cutar a Jigawa, 15 sun rasu

0

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Jigawa Abba Zakari ya tabbatar da bullowar cutar sankarau a jihar sannan ya bayyana cewa zuwa yanzu mutane 51 suka kamu da cutar inda mutane 15 suka rasa rayukan su a dalilin kamuwa da cutar.

PREMIUM TIMES ta gana da wasu iyayen da ‘ya’yan su suka yi fama da cutar inda wani mazaunin kauyen Majiya mai suna Ali Sunusi yace ya rasa ‘yar sa Khadija mai shekaru uku sanadiyyar kamuwa da cutar kwanaki uku da suka wuce.

Ya ce ya yi iya kokarin sa wajen ganin ya ceto rayuwar ‘yar sa amma hakan bai iya sa ta rayu ba.

Yau Salisu mahaifin Ummu Kulsum mai shekara 12, shima ya rasa ‘yar sa sanadiyyar kamuwa da cutar daga ‘yar zazzabin jiki da ta fara yi.

Shi ko Malam Usman ya ce bai rasa dan sa mai shekara 11 daga cutar ba sai dai ya rasa jin sa.

A karshe akalla yara 40 na kwance a asibitin Tarau sanadiyyar kamuwa da suka yi da cutar.

Kwamishina Zakari ya fadi cewa gwamnati za ta gudanar da gangamin wayar da kan mutane domin kawar da cutar a jihar.

Share.

game da Author