Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a jihar Bauchi (BSPHCDA) Adamu Gamawa ya tabbatar da rasuwar wasu mutane biyu cikin 20 din da suka kamu da cutar kwalara a jihar.
Ya sanar da haka ne ranar Litini wa manema labarai inda ya kara da cewa mutane biynu din sun rasu ne a karshen makon da ya gabata.
Gamawa yace gwamnati tare da hadin guiwar kungiyoyin bada tallafi sun tsara hanyoyin da za su taimaka wajen hana yaduwar cutar a jihar.
A karshe Gamawa yace an kebe wuri a asibitin koyarwa na Tafawa Balewa (ATBU-TH) domin kula da duka wadanda suka kamu da wannan cutar.
” Koda yake yaduwar cutar bata yi yawa ba duk da haka muna kira ga jama’a da su tabbatar suna zama cikin tsafta sannan su kula da abincin su da muhallin su don guje wa kamuwa da cutar.
Discussion about this post