CANJI: Sai Buhari ya fara canja kan sa da na mukarraban sa tukunna – Inji Bashir Tofa

0

Dan takarar zaben shugaban kasa a karkashin rusasshiyar jam’iyyar NRC, a zaben 1993, Bashir Tofa, ya soki lamirin kamfen na wayar wa jama’a kai mai take:

“Daga kaina canji zai fara.” Tofa ya ce, kamata ya yi a fara ganin canji daga kan Shugaba Muhammadu Buhari da kan mukarraban sa tukunna.

Ya ce irin wannan kamfen din ai daga sama ya kamata ya faro zuwa kasa, ba wai daga kasa zuwa sama ba, kamar yadda gwamnati ke ta hakilon aiwatarwa.

Tofa ya ce: ‘‘kamata ya yi shugabanni su fara canja kan su da kan su da kuma halayyar wadanda ke kewaye da su. Idan ba haka ba kuwa, shi ma wannan kamfen din a haka zai shiririce, kamar yadda ire-iren sa da aka yi a baya suka shiririce.”

Ya kara da cewa wannan shiri ba zai taba yin nasara ba har sai jama’a sun ga canji a cikin aljifan su, maimakon a cikin aljifan wasu tsirarun ‘yan siyasa.

Tofa ya yi wannan jawabi ne a wurin kaddamar da shirin na “Change begin with me,” a dakin taro na Gidan Gwamnatin Jihar Kano.

Ya ce irin wadannan shirye-shiryen ba su yi nasara ba a baya, saboda an saka munafurci da kuma kasawar da shugabanni na siyasa suka nuna.

A nasa jawabin Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya ce gwamnatin sa za ta yi kokari sosai wajen tabbatar da cewa ta bayar da abin koyi ga sauran jama’a domin wannan shiri ya samu nasara.

Share.

game da Author