Idan ba a manta ba, kasar nan ta sha ruguntsumin bukukuwa a dan takaitaccen lokacin da tsohon Shugaban Kasa, Marigayi Umaru Yar’Adua ya yi a kan mulki. Gwamnonin Bauchi, Zamfara da Kebbi na lokacin duk sun auri ‘ya’yan Umaru mata uku. Cikin kankanin lokaci sai ga uwargidan Umaru ‘Yar’Adua, Turai, ta zama surikar gwamnoni uku na jam’iyyar PDP a lokacin.
A yanzu kuma, tun jam’iyyar APC ba ta cika shekaru uku dindi kan mulki ba, manyan masu mulkin gwamnatin su shiga rige-rige da gasar gwangwajewar shagulgulan auren ‘ya’yan su.
PREMIUM TIMES HAUSA ta dan tsakuro wasu aurarraki da jiga-jigan gwamnatin APC suka gudanar daga hawa mulki cikin 2015 zuwa Maris, 2018.
’YAR GWAMNA BADARU DA DAN MANGAL
A ranar 30 Ga Maris, 2016 ne Lawal Mangal, da ga hamshakin tattajiri Dahiru Barau Mangal ya auri Amina, diyar Gwamna Badaru Abubakar na Jihar Jigawa. Ta na zaman ta lafiya kalau da mijin ta a Katsina. Mijinta ya auri matar sa ta farko a zamanin mulkin PDP. Yanzu kuma a zamanin APC ya kara angwancewa.
’YAR GWAMNA TAMBUWAL DA DAN MANGAL
Bayan wata daya kacal da daura auren Lawal Mangal da Amina Badaru, sai kuma aka sake shan wani ruguntsimin biki, inda kanin Lawal Mangal, mai suna Dikko ya auri Aisha, diyar Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal. A wannan biki an gudanar da shagulgula har aka shagaltu a Sakkwato.
Sai da ta kai jami’an Hisba na jihar sun kama wasu makadan a-gwangwanje a wurin bikin. Sai dai kuma gwamnatin jihar ta nuna wa Hisba fushin ta na yin katsalandan a yayin shagalin bikin.
TUNDE SABIU DA FATIMA
Tunde Sabiu Mai Taimakawa ne Na Musamman ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. A ranar 29 Ga Afrili, 2017, ya angwance da amaryar sa mai suna Fatima. A garin Kaduna. An sha shagali, kuma auren ya samu halartar jiga-jigan gwamnatin APC, har da Mataimakin Shagaban Kasa, Yemi Osinbajo.
AUREN ’YA’YAN BUHARI BIYU
Wannan dai ba ma sai an tsaya wani dogon bayani ba. Kowa ya shaida irin kasaitaccen bikin da aka yi a lokacin da Zahra Buhari ta auri dan kasaitaccen attajiri, Ahmed Indimi. Aure ne tsakanin ‘yar mai mulki da dan attajiri. Auren ne tsakanin Fulani da Barebari. Aure ne da masu akwai suka barje gumen su. Magana ta kare.
Ba a dade ba kuma Shugaban Kasa ya sake aurad da wata ‘yar sa mi suna Fatima. Bazawara ce da ta taba yin aure a Katsina, amma igiyar auren ta tsinke. Shi ma aure ne na manya. Ita ma yanzu mijin ta surikin Shuagaban Kasa ne.
’YAR OSINBAJO DA DAN BOLA SHAGAYA
Jiya Asabar aka yi wannan shagalin bikin na auren na Damilola Osinbajo, ‘yar Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo da Oluseun, dan gidan kasaitacciyar attajira Bola Shagaya. Har ma Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci bikin da kan sa. Aure ne tsakanin gidan mulki da gidan madarar kudi.
’YAR GWAMNA GANDUJE DA GWAMNA AJIMOBI
Mai karatu baya bukatar a tsaya ba shi labarin wannan auren, domin ba wanda bai san dabdalar da aka yi a bikin ba. Wanda bai samu halartar daurin auren ba, ya kalli komai a cikin wayar sa. Ango da amarya na can na shan amarci da angwanci, amma har yau labarin bikin na yawo a cikin jama’a.
AUREN GWAMNA OSHIMHOLE
Gwamnan JIhar Edo wanda ya kammala wa’adin sa ba da dadewa, Adams Oshimhole ya yi aure ya na kan gadon mulkin jihar kafin ya kammala wa’adin sa. Shi matar ta sa ma ’yar oda ce, daga wani Tsibilin Latin Amurka ya lula can ya auro ta.
Wa ya ce ba a samu samu canji a cikin canji ba? Ku gane mini hanya!