Bukin diyar Ganduje, tashin hankali ne ga musulunci da tarbiyyar ‘ya’yan mu – Sheikh Gumi

0

Fitaccen malamin addinin musulunci mazaunin garin Kaduna Sheikh Dr Ahmed Gumi ya yi tir da irin badalar da akayi a bukin diyar gwamnan jihar Kano cewa idan har Kanawa basu shiga taitayin su ba azabar Allah zai iya fado musu sanadiyyar irin haka.

Gumi ya fadi haka ne a wajen karatun sa na mako mako mai suna Dandalin Sunna in da ya kara da cewa lallai irin haka ya saba wa addinin musulunci da tarbiyya.

” Ku duba irin abin da akayi a Kano, Abin yana bani bakinciki. Diyar gwamnan ta fito tana rungumar wani kato. Sannan kuma a garinne aka hana wata ‘yar fim don ta rungume namiji. Toh ga diyar gwamnan ku ta runguma kenan yanzu za a halatta.

” Sannan ina hisbah, shugabannin da muke sa wa kenan. Wallahi kunga yadda Allah ya maida garuruwa, to wallahi garin Kano suyi hankali, da wannan fasikancin Allah zai iya halaka garin Kano. Kunga yadda Maiduguri ta zama.

Amma irin wanna ta’asa irin wannan fasadi a cikin kasa sannan babu mai yin magana kowa yayi shiru.”

Share.

game da Author