Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sake nada wasu daga cikin makusantar sa da ya hada da Boss Mustapha, Emefiele, Lawal Daura da Abba Kyari sabbin mukamai a kwamitin da zasu duba yadda za a sami yalwatar abinci a kasa da shirya manufofi domin samun nasara kan haka.
Sannan kuma kwamitin za ta samar da hanyoyin da za abi don kawo karshen rikicin makiyaya da manoma da yaki-ci-yaki-cinye wa, canjin yanayi da kare dazukar kasar nan, sace sacen shanu, yadda za a kara gina madatsun ruwa da kiwo, sannan kuma za su samar da hanyoyin da za abi wajen samarwa da kaucewa zaizayar kasa da gurbacewar magudanar ruwa da tekunan kasar nan a yankin Neja Deta da dai sauran su.
Ita dai wannan kwamiti, shugaba Muhammadu Buhari ne da kansa zai shugaban ce ta sannan za a kaddamar da ita ne ranar Litinin mai zuwa.
Mambobin kwamitin akwai gwamnonin jihohin Kebbi (Abubakar Bagudu), Taraba (Darius Dickson Ishaku), Filato (Simon Lalong), Legas (Akinwumi Ambode), Ebonyi (Dave Umahi)da jihar Delta (Ifeanyi Okowa).
Sauran sun hada da sakataren gwamnatin tarayya (Boss Mustapha); (Abba Kyari);(Babagana Mongono) da ministoci 7 da suka hada da (Audu Ogbeh); (Kemi Adeosun); (Abdulrahman Dambazau); Industry, (Okechukwu Enelamah); (Suleiman Kazaure); (Ibrahim Jibrin); da (Udo Udoma).
Sannan kuma akwai (General Abayomi Gabriel Olonisakin); (Godwin Emefiele); (Lawal Daura) (Ahmed Abubakar)da kwantorola na hukumar Shige da fice ta kasa (Mohammed Babandede).