A jiya Litinin an yi ta sa-ido a ga Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo sakon murnar cikar sa shekara 81, amma sai aka ji shiru.
Wannan rashin aikawa da sakon ya karkata daga al’adar fadar shugaban kasa, kan yadda ta ke taya tsoffin shugabannin kasa ko manyan da suka taka wata muhimmiyar rawa a cikin al’umma ko a kasa baki daya murnar zagayowar ranar haihuwar su.
Hakan ya kuma saba da yadda Buhari ya yi a shekarar da ta gabata, inda aka rika yada wasikar da ya aika wa Obasanjo ya na taya shi murnar ya cika shekara 80, har ma a cikin wasikar ya kira Obasanjo da suna, “cikakken dan kasa na duniya.”
Har ila yau, a shekarar da ta gabata, Buhari ya koda Obasanjo kuma ya cika shi da kirari duk a cikin wasikar da ya aika masa a ranar da ya cika shekara 80 a duniya.
“Irin mu da muka yi aiki a karkashin ka, mun san irin namijin kokarin da ka ke da shi, irin kaifin kwakwalwar fahimtar al’amurran da ka ke da shi, kuma ba ka yarda a raina maka wayo ba. Aiki a karkashin ka wata makaranta ce kan ta ta daukar darasi. Sannan kuma darasin da muka dauka a karkashin ka, ya kai zinari nauyin daraja.” Irin kirarin da Buhari ya yi wa Obasanjo kenan a 2017.
Ba a dai san dalilin da ya sa Buhari bai taya Obasanjo murna ba, domin Garba Shehu da Femi Adesina ba su dauki waya ba yayin da aka kira su yau da safe domin jin dalili.
Sai dai ana zaton rashin jituwar ta faru ne a baya-bayan nan da har Obasanjo ya aika masa wasika bayan ya karanta ta a bainar jama’a.