Buhari ya bude kamfanin yin siga a Neja

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjinawa masana’antar ‘Flour Mills of Nigeria’ kan gina kamfanin yin siga a kauyen Sunti dake karamar hukumar Mokwa a jihar Neja.

Bayanai sun nuna cewa an kashe Naira biliyan 50 wurin gina masana’antar a hekta 17,000 kuma za ta dinga yin ton din siga 10,000 a duk shekara sannan za ta dauki ma’aikata 10,000.

Buhari yace gina wannan masana’anta zai taimaka wajen inganta rayuwar mutanen garin musamman matasa ganin yadda kasar ta fita daga koma bayan tattalin arziki sannan gwamnatin sa zata ci gaba da taimakawa masu kokarin haka gina masana’antu kamar haka.

Share.

game da Author