Asusun tallafa wa ‘yan gudun hijira na majalisar dinkin duniya (UNHCR) ta saka yara marayu 300 a makaranta mai zaman kanta ‘Future Prowess Islamic Foundation’ a jihar Barno.
Future Prowess Islamic Foundation wata makaranta ce da Zannah Mustapha ya bude domin karantarwa da ciyar da yaran da suka rasa iyayen su a dalilin Boko Haram.
Saboda yawan yara da aka dauka a makarantar, kula da su yakan yi wahala wanda sanadiyyar haka ne yasa UNHCR ta dauki nauyin wadannan yara har guda 300 na duk abinda za su bukata da kuma abincin da za su ci.
Shugaban kungiyar Quang Bui yace UNHCRza ta ci gaba da talafawa yaran da suka rasa iyayen su da sauran mutane da suka wahala sanadiyyar hare-haren Boko Haram.
Bayan haka kwamishinan ilimi na jihar Inuwa Kudo ya jinjinawa UNHCR kan aiyukkan tallafin da take yi a jihar. Ya kuma yaba wa shugaban makarantar ‘Future Prowess Islamic Foundation’ Zannah Mustapha.
Ya kuma ce gwamnati na kokarin gina makarantu domin marayu sama da 50,000 da take kula da su a jihar sannan cikin wadannan makarantun da za ta gina za ta ba makarantar Future Prowess Islamic Foundation wasu domin rage mata wasu matsalolin da suke fama da su.