Shugabnan Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ‘yan Najeriya da ke zaune a garuruwan da Boko Haram suka kassara su ne su ka fi cancanta su auna irin kokarin da gwamnatin sa ta yi daga 2015 zuwa yau.
Buhari yayi wannan furuci ne a lokacin da ya ke karbar bakuncin tawaga daga Sarkin Saudi Arabiya, Sarki Salman a Fadar Aso Rock Villa, Abuja, jiya Alhamis.
Ya ci gaba da cewa gwamnatin sa na sane kuma ta na tafiya a bisa taka-tsantsan da alkawurran da ta yi wa al’umma a lokacin kamfen na zabe cewa za ta tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin su.
“Daga lokacin da muka hau mulki zuwa yanzu, mun yi bakin kokarin da za mu iya yi, kuma a kan turbar alkawarin da muka yi wa ‘yan Najeriya.” Inji Buhari.
Shugaban ya fada wa tawagar ta Saudi Arabiya cewa abu mafi fifikon da ya sa a gaba shi ne samar da tsaro, inganta tattalin arziki da kuma kakkabe rashawa da cin hanci.
Buhari ya yi godiya bisa gudummawa ta kwatankwacin dala miliyan goma da saudiyya ta kudirci bayarwa domin inganta rayuwar mazauna sansanonin gudun hijira a Arewa maso gabas.
Ministan Tsaro Mansir Dan’Ali ya ce tun da farko sai da tawagar ta ziyarci ma’aikatar sa sannan kuma ta yi rangadin duba-garin sansanonin gudun hira.
Shugaban tawagar, Nasir Bin Mutlaq, ya gode da irin dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, kuma ya ce an turo su ne da albishir na taimakon tallafi na dala miliyan 10 ga ‘yan gudun hijira.
Discussion about this post