A yau ne kakakin ‘yan sandar jihar Barno Joseph Kwaji ya bayyana cewa mutane biyu sun mutu sannan wasu tara sun sami raunuka a jikin su sanadiyyar fashewar bam da wasu ‘yan kunan bakin wake suka tada a Alikaramanti.
Kakakin ya bayyana cewa ‘yan kunar bakin waken sun tada bamabaman ne a lokacin da wasu sojoji dake sintiri a barikin soji na Giwa suka tsayar da su domin su bincike su, ashe daure a jikin su jigidan bamabamai ne, nan take kuwa suka tada bam din.
Hakan ya faru ne da misalin karfe 8:25 na yammacin Laraba. Su kadai ne suka mutu sai wasu kuma mutane tara da suka sami raunuka a jikin su.”
An kai wadanda suka ji raunuka asibiti.