BOKO HARAM: Kungiyar MSF ta dakatar da aiki a sansanin Rann

0

Kungiyar (MSF) ta janye ma’aikatanta dake kula da ‘yan gudun hijira sama da 40,000 a kauyen Rann, karamar hukumar Kala Balge jihar Barno.

Kungiyar ta yanke wannan shawara ne bayan harin da Boko Haram ta kai kauyen a makon da ya gabata inda mutane 11 suka rasa rayukan su kuma suka sace ma’aikatan su biyu.

Wannan sanarwa ya fito ne daga ofishin kungiyar dake Geneva.

Kungiyar MSF ta ce tun da ta fara aiki a kauyen Rann a watan Janairu 2017 take kula da ‘yan gudun hijira sama da 40,000. Ta kara da cewa za ta dawo garin Rann dinne bayan ta gamsu da tsaro a yankin.

Share.

game da Author