Hauwa Mohammed ma’aikaciyyar ICRC ce wanda ko wata daya batayi ba da fara aiki da Kungiyar agaji na ICRC a sansanin Rann.
Hauwa ‘yar shekara 25 kuma kwararriyar ma’aikaciyar Unguwar Zoma ce wanda bayan an dauke ta aiki aka tura ta Rann.
A wannan sauti da ta dauka da wayarta kuma ta tura ta WhatsApp, Hauwa na ta Inna-lillahi wa-inna Ilaihir-rajiun, tana cewa ga su nan sun zo su sace mu,amma yanzu muna barikin soja, amma zasu tafi da mu.
A haka dai suka tafi da ita da wasu bayan bata kashi da suka da sojoji.
Jami’an tsaro 11 ne suka Rasa rayukan su a arangamar.
Kalli nan: https://youtu.be/LiHGpy2wLGc