Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai yayi kira ga uwar jam’iyyar APC ta kasa da ta dai na nuna halin ko-in-kula da take yi ga matsalolin da jam’iyyar ke fama da su musamman irin wadanda ya shafi rabuwar kan ‘ya’yan da yi wa jam’iyyar Kishiya da kuma rashin yi wa jam’iyyar biyayya da wasu ‘ya’yan ta suke yi.
El-Rufai yayi wa jam’iyyar wannan gargadi ne a zaman da yayi da mambobin kwamintin da jam’iyyar ta kafa domin sasanta ‘ya’yan jam’iyyar a jihar da kasa baki daya wanda Segun Oni yake jagoranta.
Yace dole ne uwar jam’iyyar tana hukunta duk wanda ya saba wa dokar jam’iyyar ko shi waye cewa kamata yayi jam’iyyar ta hukunta irin wadannan mutane kamar yadda akayi musa a jiha.
“ Tun bayan da muka hau karagar mulki a 2015, abinda muka fara yi shine mu hada kan ‘yan jam’iyyar mu a jiha. Ni da kai na na tafi gidajen wadanda suka fadi zabe domin mu hada kai, kamar tawagar Isah Ashiru da sauransu. Haka da muka yi yasa idan ka duba zaka ga cewa akwai mutane kamar su Suleiman Abdu Kwari, Kwamishinan Kudi, Ruth Alkali Kwamshinan Kasuwanci, Ben Kure, Shugaban Hukumar SEMA da Namadi Musa na Ma’aikatar raya addina na jihar. Sannan kuma mun nada da dama daga cikin su mukamai a ofisoshin gwamnati da dama.
Sai dai El-Rufai yace nuna halin ko-in-kula da uwar jam’iyyar take yi na rashin hukunta duk wanda ya saba wa jam’iyyar ne matsalar jam’iyyar.
“ A irin haka ne munafuncin mutane irin su Suleiman Hunkuyi ya iya yin tasiri inda ya amince da shugabancin Idris Shuaibu a matsayin shugaban jam’iyyar na riko a jihar tun 2015, har ya siya masa mota, amma kwatsama a 2018 kuma ya dauko wani da aka ma manta dashi, ko shaidar zama dan jam’iyyar bashi da shi wai shine shugaban jam’iyyar wato SI Danladi na bangaren jam’iyyar da ya kafa.
“ Wani abin takaici kuma shine yadda uwar jam’iyyar ta yi burus wajen hukuntawa da tabbatar da hukuncin da jam’iyyar a jiha ta yi akan ‘ya’yan ta da suka kama da laifi.
“ Kin daukar mataki kan balankadiyar da Inuwa Abdulkadir yake ta yi a jihar domin ganin ya raba kan jam’iyyar ya nada nasa a Kaduna, kai ba Kaduna ba kawai, har da Kano da jihar Bauchi duk yasa aka sami irin wannan rashin hankali da dabban ci a jihar Kaduna.
Shi wannan SI Danladin da Inuwa Abdulkadir da ‘yan koran sa suke mara wa baya wai shine shugaban jam’iyyar a Kaduna, bashi da ko katin zama dan Jam’iyyar APC sannan kuma bai taba yin takara ba a jihar.
Daga karshe ya yi kira ga kwamitin isar da sakon sa ga uwar jam’iyyar sannan ta gaggauta daukar mataki kan abubuwan da ya zayyano.