BAKON DAURO: Gwamnatin Enugu za ta yi wa yara 500,000 allurar rigakafi

0

Mataimakiyar gwamnan jihar Cecelia Ezeilo ta bayyana ce wa gwamnatin jihar za ta yi wa yara 500,000 allurar rigakafin cutar Bakon Dauro a fadin jihar.

Ezeilo ta sanar da haka ne ranar Litini inda ta kara da cewa gwamnati na sa ran yi wa yara ‘yan watanni tara zuwa shekara biyar rigakafi tsakanin wadannan ranaku da ta kebe.

” Haka ne kawai zai taimaka wajen ceto rayukan yaran mu da kuma kare su daga kamuwa da bakon dauro.”

Ezeilo ta kuma kara da cewa gwamnati na kokarin hada karfi da karfe da masu ruwa da tsaki da kungiyoyi don ganin ta kawar da cutar daga jihar gaba daya.

Bayan haka kwamishinan kiwon lafiya Fintan Ekochin ya bayana cewa an tsara shirin yadda kowani yaro zai sami yin allurar ko da yaron ya taba yi ko bai taba ba.

” Rahotanin kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ya nuna cewa yi wa yara allurar rigakafi ya taimaka wajen ceto rayukan yara 2,000 daga mutuwa a shekarun 2000 zuwa 2015.”

Share.

game da Author