Shugaban Kiristoci Mabiya Darikar Katolika na Duniya, Pope Francis, ya bayyana cewa masu tafka manyan zunubai su kwantar da hankalin su, ba za su dandana kudar wutar jahannama ba.
Haka Fafaroma ya fada a cikin wata hira da aka yi da shi yau Alhamis a jaridar La Repubblica ta kasar Italiya.
“Duk wanda ya tuba idan ya mutu, to idan ubangiji ya yafe masa, shikenan. Wadanda ba za a iya karbar tubar su ba kuma, kawai sai dai ran na su ya bace kawai shikenan.
“Babu wani wuri wai jahannama – abin da ke akwai dai shi ne bacewar ruhin masu manyan zunuban da ba a iya yafe musu.” Inji shi.
Ba a yi mamakin wannan hira da jaridar ta yi da shi ba, musamman ganin cewa shi kan sa wanda ya yi hirar da shi, wani tsohon dan jarida ne mai suna Eugenio Scalfari, wanda bai yarda akwai Allah ba, kuma ya na samun shiga sosai a wajen Fafaroma din fiye da kima.