Kungiyar Musulmi MURIC ta ce ba za ta amince da sabuwar jadawalin jarabawar WAEC ba duk ta canza ranar rubuta jarabawar Chemistry da ta ke korafi akai cewa an saka jarabawar ranar Juma’ah.
Shugaban Kungiyar MURIC, Ishaq Akintola ya bayyana cewa dalilin da ya sa musulman Najeriya ba za su yarda da haka ba shine ganin cewa akwai wasu jarabawar da ba a canza lokuttan rubuta su ba ranar, suna nan a ranar Juma’ah.
A makon da ya gabata Musulmin kasar nan sun soki lamirin Hukumar Shirya Jarabawar kammala Sakandare (WAEC) kan yadda ta shirya za a rubuta jarabawar Chemistry a daidai lokacin sallar Juma’a.
Ishaq ya bayyana cewa jadawalin jarabawar bai yi wa musulmi adalci ba.
Ya kuma kara cewa hakan na yin nuni da yadda ake tauye wa musulmi hakki da ‘yancin su a kasar nan.
“ Matsawar aka ce babu adalci, to zaman lafiya ba zai taba samuwa ba. Shi ya sa kowa ke ta hankoron a samu wanzar da zaman lafiya.”
Hukumar ta WAEC ta ce sauran jarabawar da bata canza lokuttan su ba ba zai hana masu yin Sallah samun Sallah ba ranar Juma’ah.
Ishaq Akintola ya ce Kungiyar kare hakkin Musulmin na MURIC ba za amince da wani shiri ba Idan ba daraja ranar Juma’ah WAEC din tayi ba ta canza duk jarabawar da zai Iya hana dalibai samun Sallar Juma’ah.