Ba a bar mu mun fayyace wa Buhari yadda aka sace mana ‘ya’ya ba –Iyayen daliban Dapchi

0

Iyayen daliban Sakandaren Dapchi da Boko Haram su ka sace, sun bayyana takaici da haushin yadda aka hana su yin magana gamsasshiya a gaban Shugaba Muhammadu Buhari, yayin da ya kai ziyara a garin jiya Laraba.

Jiya ne dai Shugaban Kasa da ministoci tare da gwamnonin Yobe da Barno, suka isa garin Dapchi da misalin karfe 4:00 na yamma.

Iyayen daliban da aka sace tare da shgabannin yankin ne suka tarbe su yayin da suka isa garin.

Haka shugabar makarantar da shugaban iyayen yaran sun yi takaitattun jawabai ga shugaban kasa a kan yadda harin ya faru har aka gudu da ‘ya’yan su.

Daga nan kuma sai shi ma shugaban kasa ya yi musu jawabi a cikin wani dakin taron sakandare din ta Dapchi.

” Da yardar Allah za mu duk abin da za mu iya yi domin mu kawo zaman lafiya da cin hanci da rashawa a kasar nan, kuma mu na ci gaba da yin hakan.

“Da yardar Allah mun tura dakarun sojojin mu a cikin gida da waje na sojoji da sojojin sama har ma da ruwa cewa su yi duk iyakar kokarin su domin a ceto wadannan dalibai kuma a dawo muku da su.’

Sai dai kuma shugaban iyayen da aka sace wa ‘ya’yan mai suna Bashir Manto, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ba su ji dadin yadda shugaban kasa bai samu damar tattaunawa da su a tsanake ba.

Amma sun ce sun gamsu da yadda ya jajanta musu, kuma ya kara musu kwarin guiwa da ya ce ba za su sarara ba har sai an dawo da daliban.

Share.

game da Author