Atiku ya roki ‘yan Najeriya da su zauna lafiya da Juna

0

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma jigo a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya yi tir da rikicin da aka yi a jihar sa ta Adamawa inda ya yi ajalin mutane 13 wanda cikin su akwai kakakin jam’iyyar PDP na jihar Sam Zadock.

Atiku ya bayyana cewa halin da kasa Najeriya ta shi na kashe-kashen rai abin takaicine ga kasar nan. Ya ce mutane sam basu da tausayi a zukatan su sannan sun bari son rai ya yi musu katutu a zuciya.

Ya dangana irin wannan hali da kasa ta shiga ciki da rashin shugabanci nagari.

A ranar 28 ga watan Faburairun ne kakakin jam’iyyan PDP Sam Zadock da wasu mutane 12 suka rasa rayukan su a rikici tsakanin makiyaya da manoma a kauyukan Numan da Demsa dake jihar Adamawa.

Bayanai sun nuna cewa Zadock da mutane 12 sun rasa rayukan su ne da suka fada wani tarko da Fulani suka yi wa mutanen kabilar Bachama don taukar fansar kisan da akyi wa wasu ‘yan uwan su.

Atiku ya roki jama’a da su zauna lafiya da juna sannan yayi kira ga gwamnati da ta maida hankali wajen ganin ta samar wa matasa aikin yi don gujewa irin haka.

Share.

game da Author