Atiku ya roki magoya bayan sa da su yanki katin rajista

0

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yi kira ga daukacin magoya bayan sa, da su garzaya kowa ya yanki rajistar zaben 2019.

An dai fara rajista tun daga cikin watan Afrilu, 2017, kuma ba za a daina ba. Sai ana saura kwanaki 60 a fara zabe.
Atiku ya yi wannan kira ne a wurin kaddamar da wata kungiyar yakin neman zabe da magoya bayan sa, mai suna Concern Citizens For Atiku.

Kungiyar ta kuma kaddamar da shafin ta na intanet.

Atiku, wanda shugaban kungiyar magoya bayan sa mai suna Oladimeji Fabiyi ya wakilta, ya bayyana cewa ya lura fasahar zamani ta taka muhimmiyar rawa wajen janyo hankulan jama’a ga shiga tsamo-tsamo cikin harkokin zabe.

Sai dai kuma ya kara yin jan hankalin cewa to fa shi zabe ba a soshiyar midiya ake yin sa ba, sai an tashi an yanki rajista, kuma sai an fita ranar zabe an jefa kuri’a.

Atiku ya kuma hori matasa su tashi tsaye hakan a yi fafutikar mukamai da su, domin su kwace siyasa daga hannun tsoffin ‘yan alewa. Ya ce kuma ya na da muradin taimaka musu a kan haka.

Share.

game da Author