A wani gagarimin shiri da jam’iyya mai mulki ke yi domin cin zaben 2019, ko ana ha maza ha mata, APC ta ware kasafin kudi har na naira biliyan 14.82 da za ta yi aikace-aikacen jam’iyya da su a cikin 2018.
Shirin kashe wadannan makudan kudade har kusan naira biliyan biyar, ya na kunshe ne a cikin wata takarda da Ma’ajin Jam’iyyar APC na Kasa, Bala Gwagwarwa ya raba wa jigajigan jam’iyya, kamar yadda jaridar Punch ta ranar Asabar ta ruwaito.
Wasu ayyukan da za a gudanar daga cikin wadannan kudaden, APC za ta kashe naira biliyan 1.96 wajen gina hedikwatar jam’iyya ta kasa a Abuja, sai kuma naira biliyan 1.3 da za a kashe wajen taron gangamin jam’iyya, da sauran wasu ayyuka da dama.
Za a raba wa jihohi da shiyyoyi naira biliyan 2.48. yayin da za a kashe naira miliyan 500 wajen samar da motocin zirga-zirga. Wajen harkar gudanar da zabe a taron gangami kuma za a kashe naira miliyan 400.
APC ta ce za a samu wadannan kudaden da za a kashe ne ta hanyar saida fom ga masu sha’awar tsayawa takara, kafa gidauniyar neman gudummawa, haraji kan masu rike da mukamai da kuma kudin cinikin katin shaidar dan jam’iyya da za a saida wa magoya bayan bayan APC a kasa baki daya.
Discussion about this post