Jim kadan bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Sanata Bola Tinubu shugabancin kwamitin sasanta rigingimun cikin jam’iyyar APC, babban jigon na jam’iyyar ya shiga taron sirri da Buhari, kafin ya kai ziyara a hedikwatar jam’iyyar ta kasa a karon farko tun cikin 2015 bayan an ci zabe.
Daga nan kuma sai ya shiga gudanar da taruka da manyan ‘yan jam’iyya a Abuja, irin su Shugaban Malajisar Dattawa, Bukola Saraki, Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje da Sanata Rabi’u Kwankwaso.
Tinubu ya je wasu jihohin da ake ganin cewa tutar APC ta kama wuta sosai kamar jihohin Kano da Kaduna.
Tawagar Tinubu ta kuma je Sokoto inda ta gana da Gwamna Tambuwal, Sanata Aliyu Wamakko da Inuwa Abdulkadir, mataimakin shugaban jam’iyyar APC shiyyar Arewa-maso-Yamma.
Daidai lokacin da ya fara wannan rangadi, Tinubu ya fara cin karo da matsala da shugaban APC na kasa, John Oyegun, wanda ya zarga da yi masa makarkashiya, abin da har sai da ta kai shi ya rubuta wa shgaban kasa wasikar gargadin Oyegun.
Alamomi sun nuna tun bayan wannan wasika da ya rubuta a fusace, guyawun sa sun fara sanyi daga zumudin gudanar da aikin da Buhari ya dora masa na magancewa da sasanta matsalar APC ganin ga zaben 2019 na matsowa.
Tun bayan taro da jiga-jigan APC suka yi na kwanaki uku a hedikawatar a Abuja, har yau Tinubu bai sake yin wani taron sasantawa da kowane bangare ba.
A yankin Arewa-maso yamma ne APC ta fi samun kuri’u masu dimbin yawa a 2015, amma kuma sai jam’iyyar ta yi sakaci ta shiga ruguguwar rikici, har ya kai ya munana sosai.
Hakan kuwa na nuni da cewa akwai rikita-rikitar da kwamitin Tinubu ba zai ya sasantawa kenan.
KANO: GANDUJE DA KWANKWASO
A Kano dai Ganduje da Kwankwaso ba a ga-maciji. Kwankwaso ya daina shiga duk wata harka ta APC a kasa da jiha. Ko zuwan da Buhari ya kai ziyara a Kano Kwankwaso bai je ba. Ya yi yinkurin zuwa ganin gida a farko zuwan sa na biyu Kano tun bayan da aka zabe shi, amma aka ba shi shawara ya janye saboda gudun tashin hankali.
Ganduje da Kwankwaso na ta antaya wa bangaren juna kalaman da har tashin duniya gaba ta shiga tsakanin su. Magoya bayan Kwankwaso na cewa babu sulhu.
Sun zargi Buhari da komawa bangaren Ganduje, wanda hakan alama ce da ta nuna ya goyi bayan komawar Sanata Lado cikin APC daga PDP.
Idan aka takura wa Kwankwaso da magoya bayan sa za su yi anti-party a Kano da sauran garuruwa. Har yanzu magoya bayan Kwankwaso na cizon yatsan saran su da aka yi a lokacin hawan Sallah a Kano.
Kwankwaso na da karfi a Kano sosai. Shi ne Sanatan da ba a taba samun sanatan da ya taba samun kuri’u yawan nasa ba a tarihin zaben Najeriya.
KADUNA: EL-RUFAI, SHEHU SANI DA HUNKUYI
Kamar yadda ta rikice a Kano, haka ta rikirkice a Kaduna. Wutar rikici ce da ke ci ganga-ganga mai harshe hudu.
Harshen a farko akwai rikicin Gwamna El-Rufai da SANATA Shehu Sani, sai El-Rufai da Inuwa Abdulkadir, El-Rufai da Sanata Hunkuyi da kuma El-Rufai da talakawa ko a ce jama’ar jihar.
Rushe gidan Hunkuyi da na Inuwa Abdulkadir ya dagula kuma ya rikita jam’iyyar. Amma babbar matsalar ita ce rikicin gwamna da Shehu Sani da kuma na jama’ar gari da ke kallon tsare-tsaren da gwamnan ya shigo da su, duk na kuntata wa jama’a ne, sabanin alkawarin kawo sauki da jam’iyyar APC ta yi kafin ta hau mulki.
ZAMFARA: GWAMNA YARI DA SANATA KABIRU MARAFA
Wadannan jiga-jigan ‘yan jam’iyya biyu sun raba rana a kullum damben zafafan kalamai ne kan juna ke fitowa daga bakin su. Tun daga lokacin da Gwamna Abdul’azir Yari ya rubuta wa Shugaba Buhari takardar rashin amincewa da nada Ahmed Mahmood a matsain kwamishinan tarayya na INEC, an rika samun sabani a tsakanin su.
Yayin da gwamna Yari ba ya gajiya da yawon rashin zama jihar, shi kuma Sanata Marafa ba ya gajiya wajen caccakar sa.
Ya sha fitowa karara ya na sukar gwamnan ya na cewa rashin zaman da ba ya yi ne ya haddasa yawan kashe-kashen da ake yi a jihar.
Da ya kai ziyarar jaje fadar Sarkin Zurmi, Marafa ya ce gwamna Yari ya san dukkan masu kashe-kashe a jihar Zamfara.
KOGI: GWAMNA YAHAYA BELLO DA DINO MELAYE
Na su rikicin ya zama gaba sosai a kullum kowa zargin kowa ya ke da neman ganin bayan sa. Dino ya matsa wa Bello saboda ya na ganin shi ya kitsa hayaniyar yi masa kiranye. Shi kuma Bello ya yi ta kokarin ganin koma-bayan Dino Melaye.
Hatta wani yinkurin kama Dino da aka yi cikin makon da ya gabata, ya ce aikin gwamna Bello ne, shi ya tura su.
ADAMAWA DA SOKOTO
Su ma suna cikin rikici, amma dai ba kamar na irin jihohin Kano da Kaduna ba. Adamawa gwamna Jibrilla Bindow na kikiniya da bangaren tsohon gwamna Murtala Nyako.
Discussion about this post