A ranar Asabar din da ya gabata ne gwamnatin jihar Kebbi ta daura wa zaurawa 100 aure a jihar.
Gwamnatin jihar Kebbi da karamar hukumar Argungu suka yi wa wadannan mata aure a fadan sarkin Argungu Samila Mera.
Gwamnati tace anyi haka domin rage tazurai, gwawraye da mata zaurawa da ke bukatan haka amm basu da kudin yi, sannan da sama musu matsuguni na sunna.
Da yake tofa albarkacin bakin sa a wurin, sarkin Argungu ya yi kira ga iyaye da su daraja aure kuma su dunga ganin aure a matsayin matakin rage yawan mata da basu dashi a cikin al’umma.
” Aure ibada ne kuma zaman hakuri a aure ne kawai hanyar samun albarka a cikin sa.”
Cikin kayayyakin da ma’aurantan suka samu sun hada da kayan lefe, Naira 30,000 kudin jari, turamen zannuwa da dai sauran su.
Discussion about this post