An yi jana’izar marigayi Wakil

0

Bayan sanar da rasuwar Sanata Ali Wakil da safiyar Asabar din yau, da misalin karfe 2 na rana akayi masa sutura aka kai sa makwanci a makabartar dake Unguwar Gudun Abuja.

Ali Wakil ya yanke jiki ne ya fadi bayan ya kammala shiri tsaf zai tafi daurin aure Yola, tun daga nan ko ashe Allah ya dauke abin sa ne.

Ya rasu ya bar yaya da mata biyu.

Cikin wadanda suka halarci jana’izan marigayi Wakil sun hada da Shugaban majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki, Sanata Dino Melaye, Sanata Godswill Akpabio, Ministan sufuri, Rotimi Amaechi da ‘yan uwa da abokan arziki.

Share.

game da Author