An karrama Rahama Sadau a Amurka

0

Kungiyar ‘Women Illuminated Film Festival Parallel to United Nations’ ta karrama fitacciyar ‘yar wasan finafinan Najeriya, Rahama Sadau.

Wannan Karramawa dai shine na farko da wata ‘yar wasar fim a Arewacin Najeriya za ta taba samu.

Da take bayyana farin cikin ta a shafin ta na Instagram, Rahama ta ce ” Ban san yadda nayi na ga kai na a wannan matsayi da ba za ta ba, lallai zan ta ba mantawa shi ba a rayuwata. Ina mai matukar farinciki.”

Rahama Sadau ta zama zakarar gwajin dafi sannan abin alfahari ga mata musamman masu tasowa da sha’awar shiga harkar finafinai da shakatawa sannan kuma ita ce mace ta farko ‘yar Arewa da ta shiga jerin mata 10 da suka fi shahara a Najeriya.

Share.

game da Author