Rundunar ‘yan sandan jihar Barno ta kama wani saurayi mai suna Musa Faisal da laifin zuba wa buduwar sa Fatima Usman mai shekaru 26 ruwan batir a fuska.
Kwamishinan ‘yan sandan Damian Chukwu wanda ya sanar da haka ranar Alhamis wa manema labarai a Maiduguri yace hakan ya faru ne sanadiyyar rashin aura wa Faisal masoyiyar sa Fatima a matsayin mata da iyayen Fatima suka yi.
” Ko da iyayen Fatima suka ki amince da Faisal hakan bai hana wadannan masoya ba haduwa a boye.”
Chukwu yace da Faisal ya gaji da haduwa da Fatima a boye sai suka yi shawara da abokin sa mai suna Muhammed Babangida da su ci mutunci Fatima.
” Abokan sun far wa Fatima ranar 16 ga watan Maris da wannan ruwan batir yayin da take hanyar ta na zuwa wurin da suka saba haduwa da saurayin ta Faisal inda wajen watsa mata ruwan batir din ya zuba wa Faisal a jiki.”
Ya ce rundunar ta gano haka ne a binciken da ta gudanar a kan Faisal da abokin sa Babangida sannan da zaran sun kammala binciken za su shigar da kara kotu.
Bayan haka Chukwu ya kara sanar da cewa rundunar ta kama wasu mutane biyu da suke da alaka da kisan wata karuwa mai suna Precious Needy mai shekaru 28 da aka tsinci gawanta a gidan saukan bakin ‘Galaxy Hotel’ dake Galadima a Maiduguri.
Ya ce mutanen da suka kama sun hada da Yakubu Luka mai shekaru 39 da Amelia Ka’anfsa mai shekaru 26.
Ya ce Yakubu mai gadi ne a gidan saukan bakin sannan Ka’anfsa makwabcin Precious ne a inda take zama sannan bayan sun kammala gudanar da bincike a kan su za shigar da kara a kotu.