An kama daya daga cikin wadanda suka yi garkuwa da wasu ‘yan mata biyu a Kaduna

0

PREMIUM TIMES ta rawaito yadda wasu ‘yan fashi da makami suka azabtar da wasu ‘yan mata biyu da suka sace daga gidan wani Malam Haliru a kauyen Tashan Jirgi dake karamar hukumar Igabi jihar Kaduna.

A hiran da ‘yan matan suka yi da PREMIUM TIMES sun bayyana cewa barayin sun afko gidan su ne da misalin karfe 2 na dare ranar Lahadin da ya gabata inda suka bukaci kudi da sauran ababe masu daraja daga wajen iyayen su.

” Yayin da muke barci a cikin wannan dare sai muka ji muryar wadannan barayi da suke kokarin karban wayoyi da kudi daga hannun mahaifin mu da matar sa sannan suka ce musu basu da kudin da za su basu.

” Fadin haka da mahaifin mu ya yi ne ya sa wadannan barayi suka tafi da mu sannan suka fada masa cewa duk lokacin da ya basu kudaden da suke bukata za su sako mu.”

‘Yan matan sun ce barayin sun kai su cikin wani daji inda suka yi musu fyade, suka lakada musu duka sannan suka jefa su a cikin wani rami har safe.

” Da garin Allah ya waye sai barayin suka kira mahaifin mu bayan sun karbi lambar wayar sa daga hannun mu suka kira shi sannan suka bukaci ya biya Naira miliyan daya kafin su sako mu.”

Daya daga cikin ‘yan matan ta ce za ta iya gane maza hudu cikin barayin amma wasu guda biyu da suke gadin su da dare ne ba za ta iya gane su ba.

Bayan haka mahaifin su Malam Haliru yayin da yake tabbatar mana cewa sai da ya je ya ajiye musu wannan kudi a gindin wata itaciya a dajin sannan ‘ya’yan sa suka dawo gida.

” Na shawarci ‘ya’yana da su hakura su ga wannan abu da ya same su a matsayin gwaji ne daga wajen Allah.”

Malam Haliru ya ce wasu daga cikin matasan da suka tayi shi bin diddigin wannan abu, sun faki inda aka ajiye kudin sannan sun samu sun kama daya daga cikin barayin wanda ‘yar sa ma ta gane shi.

Share.

game da Author