An kama barawon kaya da abinci na tallafi a sansanin ‘yan gudun hijra dake Maiduguri

0

Rundunar ‘Civil Defence Corps ‘(NSCDC) na jihar Barno ta bayyana cewa ta kama wani barawon takardun da majalisar dinkin duniya (UN) ta bada domin yaran da ke karatu a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke jihar.

Rundunar ta kara da cewa ta kama wasu katan – katan na abincin da kungiyar ‘World Food Programme (WFP) ta bada domin ciyar da yaran jihar dake fama da matsinacin yunwa duk a jihar.

Shugaban rundunar Ibrahim Abdullahi ya sanar da haka ne ranar Litini wa manema labarai a Maiduguri sannan ya kara da cewa idan kungiyoyin bada tallafi sun kawo kayan agaji irin haka wasu mutane kan je su sace kayan ko kuma su siya kayan arhan banza sannan su fitar da su jihar domin a canza musu fasali yadda idan sun dawo da su cikin jihar suna saidawa babu wanda zai iya ganewa ballantana kuma a kamasu.

Ya ce jami’an sa ba za su kyale duk wanda suka kama yana aikata irin haka, sannan za su sa ido sosai don ganin hakan bai sake faruwa ba.

Share.

game da Author