An kafa dokar hana walwala a karamar hukumar Bassa, jihar Filato

0

Sanadiyyar rikicin da yaki ci yaki cinyewa a karamar hukumar Bassa gwamnatin jihar Filato ta kafa dokar hana walwala a yankin.

Sakataren gwamnatin jihar Rufu Bature ya sanar da haka ranar Laraba inda ya ce an kafa wannan doka ne domin hana ci gaba da rikicin da ake ta fama da shi a yankin.

Idan ba a manta ba a ranar Talatan da ya gabata ne wasu ‘yan bindiga suka far wa mazaunan karamar hukumar Bassa inda mutane 25 suka rasa rayukansu.

Bayan haka ranar Laraba wasu kuma mahara sun kai wa kauyen Dong hari inda mutane uku suka mutu sannan aka kona gidaje 11 da motoci hudu a kauyen

Dokar ta hana mutanen yankin fitowa da karfe shida na safe zuwa shida na yamma sannan gwamnatin ta kafa jami’an tsaro don ganin anyi biyyaya da dokar.

Share.

game da Author