Mai taimaka wa gwamnan jihar Kwara kan harkokin yada labarai Muyideen Akorede ya bayyana cewa gwamnati ta kafa dokar hana kiwon dabbobi da dare a jihar.
Ya sanar da haka ne da yake zantawa da manema labarai ranar Talata bayan kammala taron majalisar tsaro na jihar a garin Ilorin.
” Wannan shawara da muka dauka zai taimaka wa jami’an tsaro wajen samar da tsaro da kuma gane masu tada zaune tsaye a jihar.” Inji Gwamna Ahmed.
Cikin wadanda suka halarci wannan zama sun hada da mambobin kungiyar makiyaya na Miyetti Allah, kungiyar manoma, sarakunan gargajiya, shugabanin kananan hukumomi da masu ruwa da tsaki a jihar.